Kano – Al’ummar Kano Ta Arewa sun bayyana farin cikinsu da godiyarsu ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin (Maliya), CFR, bisa ƙoƙarinsa na ganin an gabatar da ƙudirin kafa Federal Medical Centre (FMC) Gwarzo a Jihar Kano.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa idan aka samu wannan cibiyar lafiya, za ta taimaka wajen sauƙaƙa wahalhalun da marasa lafiya ke fuskanta wajen neman ingantaccen magani a manyan asibitoci da ke nesa. Sun ce cibiyar za ta kuma samar da guraben aikin yi, ƙarfafa horar da ma’aikatan lafiya tare da bunƙasa bincike da ci gaban fannin kiwon lafiya.

Al’ummar sun ce wannan yunƙuri ya ƙara nuna irin jajircewar Sanata Barau wajen kawo ayyukan ci gaba da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye, musamman a Kano Ta Arewa.

A ƙarshe, sun yi addu’ar Allah Ya ba shi lafiya, hikima da ƙarfin guiwar ci gaba da wakiltar al’umma tare da ganin an kai ƙudirin zuwa matakin aiwatarwa domin al’ummar yankin su amfana da wannan muhimmin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kotun Bebeji Ta Gurfanar da Mutane Biyu Kan Sayar da Naman Wata Saniya

Daga: Dantala Uba Nuhu Kura Kotun Majistare mai Daraja ta Ɗaya da…

Yanda El-Buhaj Royal Academy Ta Hada Ilimi Da Koyon Sana’o’i, Ta Fara Fidda Dalibai Masu Dogaro Da Kansu

Daga: Kabir Getso ‎Baya ga ingantaccen Ilimi da Dalibi zai samu a Makarantar…

Mataimakin Gwamna Ya Gana Da Karamin Ministan Gidaje A Abuja

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Karamin ministan gidaje da raya birane Rt. Hon.…

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Sabon Sharaɗi Na Buɗe Asusun Banki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani sabon mataki da zai shafi dukkan…