Daga: Garba Musa Yakasai
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da yunkurin neman sabon bashin dala biliyan 1.25 daga Bankin Duniya domin habbaka tattalin arziki, bunkasa zuba hannun jari da kuma samar da ayyukan yi a fadin kasar nan.
Bashin, wanda aka kiyasta ya kai kusan tiriliyan ₦1.7, na daga cikin manyan kudaden tallafin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke nema domin ci gaba da aiwatar da manufofin farfado da tattalin arzikin kasa.

Rahotanni daga jaridar Punch sun nuna cewa idan aka amince da bashin, kudin da aka kiyasta ya kai kusan tiriliyan ₦1.7, zai kasance daya daga cikin manyan bashin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu tun bayan hawanta mulki.
An bayyana cewa gwamnatin na kokarin amfani da bashin wajen habaka tattalin arziki, karfafa bangaren masu yanayi mai kyau da kuma samar da damar ayyukan yi domin rage matsin rayuwa da talauci da ke addabar al’umma.

Idan aka amince da sabon bashin, ana hasashen jimillar bashin Najeriya zai haura tiriliyan ₦160, abin da ke kara tayar da hankalin jama’a kan makomar tattalin arzikin kasar da kuma nauyin biyan bashin da ke kara hauhawa.