Daga: Kabir Getso
Akwai Bukatar likitoci su daina kwarara zuwa kasashen ketare Don gudanar da aiyukan su, sakamakon Bukatarsu a cikin Kasar nan.
Bukatar Hakan ta fito ne ta bakin Shugaban Babban Asibitin Karamar hukumar hadejia dake Jihar Jigawa
Dr. Habib Abubukar a lokacin da yake ganawa da manema Labarai a ofishinsa.
Ya kara da cewar sanin kowa ne dai likitoci da dama a kasar nan na tserewa zuwa kasashen ketare,domin cigaba da gudanar da aiyukan su akasashen waje,duba da irin yadda kasashen wajen ke sauke dukkan nauye-nauyen da suke bukata,Wanda gida najeriya a cewar war su likitocin sun gaza cimma bukatun su,
Dr. Habib Abubukar shine shugaban babban asibitin karamar hukumar hadeja dake jahar jigawa ya bayyana cewa shi baya daya daga cikin likitocin da zai Kasarsa ya tsallaka kasashen ketare, sakamakon yadda gwamnatin jahar jigawa ta tallafa masa har ya zama likita Mai cikakken iko,Hakan yasa yace ba inda zai je ya bada gudunmuwar da ta dace a harkokin lafiya irin jaharsa.

”Indai har Gwamnati zata baka kyakkyawan gudunmuwar karatu da tallafi wasu lokutan ma da daukar nauyin karatun na Lafiya har ka kammala to babu hujjar da zata sa bayan ka kammala ka gudu kasar waje bayan ana bukatar taka a kasarka”
Inji Dr. Habib.
Dr. Habib ya kuma godewa Mai girma gwamna mal. Umar namadi Dan modi bisa namijin kokari da yake akan harkokin daya shafi lafiya Wanda har wasu jahohi na amfana da kulawar.
Sannan, Dr. Abubakar yayi kira ga likitoci dasu Mai da hankali wajen kula da marasa lafiya,da kuma kula da hakkin aikin.