Daga: Dantala Uba Nuhu
Alh Rabiu Abubakar Suleman Babina ya mika gudunmawar Gaggawa ta magungunan rugakafin kamuwa da cututtuka masu saurin yaduwa ga babban asibitin karamar hukumar ta Kura.
Hakan ya samo asali ne da samun labarin bullar cutar (Lassa) wadda wata mata ‘Yar asalin garin Makwaro a karamar hukumar Garun-Malam ta jamu da cutar yayin da ‘yan uwanta cikin gaggawa suka kaita babban asibitin karamar hukumar ta Kura.
Daga bisani likitocin asibitin suka gudanar da kwakkwaran bincike da gwaje-gwaje har suka gano wannan matar ‘yar Garun Makwaro dake yankin Hukumar ta Garun-Malam tuni har ta kamu da cutar ta Lassa. Bayan binciken da kadan Allah yayiwa matar rasuwa acikin asibitin.
Haka zalika, aakilinmu ya tabbar mana da samun labarin cewar me gidanta shima ya kamu da waccan cuta ta (Lassa), aantda yanzu haka yana daya daga cikin asiibitocin da gwamnatin Jaha ta kebe dan bawa masu irin wadannan cututtuka agajin gaggawa domin killace shi.
Saidai, shugaban karamar hukumar ta Kura ya halarci babban asibitin dan kaimasu agajin gaggawa na magungunan.
A yayin ziyarar ne yana tare da Daraktan Mulki na karamar hukumar Alhaji Sabo Muhammd, shugaban sashin lafiya Alh Sani Abdullahi ‘Bagwai da sauran Shugabannin sassa da Kansiloli.
Tunda farko a jawabinsa, shugaban karamar hukumar ta Kura, ya bayyana makasudin zuwansu asibitin da bayar da managartun shawarwari ga al’umma tare da yiwa kafatanin ma’aikatan babban asibitin na karamar hukumar ta Kura godiya bisa jajircewarsu inda yace “na jinjinawa kwarewarku, kuma mun gode kwarai dan ganin andakile yaduwar wannan cuta, da kuma ganin irin dawainiyar da ma’aikatan asibitin keyi da majinyatan dake cikin wannan asibiti.”

Shugaban sashin lafiya na karamar hukumar ta Kura Sani Abdullahi ‘Bagwai, ya bayyana yawan magungunan da aka kawo ma asibitin.
Daga bangaren shugaban babban asibitin na Kura, Dr. Imrana ya bayyana yanda suka sami waccan matar ta garin Makwaro lallai na dauke da cutar Lassa. Kuma ya mika Kokon bararsu wurin shugaban Karamar Hukumar dama gwamnatin Jaha dan ganin ankara kawowa asibitin dauki.
Wani cigaban kuma, wakilin namu na ziyarci ofishin shugaban Karamar Hukumar Garun-Malam din Barr. Aminu Salisu bayanan sai dai ya gana da wakilinsa Kansilan Dakasoye Honorabul Aliyu Abdulhamid. Inda daga bisani babban Limamin Kauyen Makwaro Imam Abdulmumin Alkasim shima yayi karin haske Kan yanda ya sami labarin kamuwar matar da wannan cuta me saurin yaduwa bayan rasuwarta.