Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa

A kokarinsa na inganta rayuwar matasa da bunkasa ci gaban kasa, Shugaban shirin tallafin gwamnati mai suna Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP), Hon. Hamza Ibrahim Baba, ya bayyana kudirinsa na daukar nauyin horas da matasa 55 a fadin Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano, a fannin koyon fasahar zamani (digital skills acquisition).

Hon. Hamza Ibrahim Baba ya bayyana hakan ne a yayin taron kolin matasa (Youth Summit) da National Youth Council of Nigeria (NYCN) reshen karamar hukumar Dawakin Tofa ya shirya, a ranar 6 ga Yuli, 2025.

“Ya umarci shugabannin kungiyar NYCN da su fitar da jerin sunayen matasa 55 da za su ci gajiyar wannan horo, daga kowane yanki na mazabu 11 dake karamar hukumar, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba. Ya bayyana wannan mataki a matsayin hanya ta gaskiya don samun ci gaba, tare da sha alwashin yin aiki kafada-da-kafada da shugabannin kananan hukumomi da na jihohi domin habaka shirin GEEP da kuma ci gaban kasa baki ɗaya”.

Baya ga haka, Hamza Baba ya kuma dauki nauyin tallafawa aikin buga littattafan rubutu da kungiyar NYCN ta fara aiwatarwa, domin habaka ilimi a yankin Dawakin Tofa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Tinubu Zai Yi Wa Shugabannin Duniya Jawabi A Taron MDD Na 81

Daga: Abdullahi Bashir Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi a gaban…

Shugaban K/H Birnin Kano, Salim Hashim, Ya Taya Al’umma Musulmi Murnar Shigowar Sabuwar Shekarar Hijira ta 1447

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu    Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim…

Tinubu Ya Taya Rediyon Tarayya Murnar Cika Shekaru 75, Ya Jaddada Muhimmancinta A Kasa

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya mahukunta…

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Mutanen 15 Domin Duba Aikin Kaga Kwalejin Fasaha A Garin Gaya

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin fasaha…