Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar ‘yan kasuwar kayayyakin masarufi ta kasa, reshen jihar Kano, ta bukaci Gwamnatin jihar Kano da ta tallafa mata da jari domin kara habaka ayyukanta da kuma ci gaban ‘yan kasuwar.

Mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Auwalu Allah Ya Tsare, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke kasuwar Singa.

Alhaji Auwalu ya jaddada kudirin kungiyar na marawa Gwamnatin jihar Kano baya a fannoni daban-daban, yana mai yabawa gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yadda take aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a sassan jihar.

Ya ce duk wanda ya duba irin ayyukan da gwamnatin ke gudanarwa zai tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alkawuran da ya daukar wa al’ummar Kano na samar da ayyukan da za su bunkasa tattalin arzikin jihar.

A sakamakon haka, ya yi kira ga Gwamnatin jihar Kano da ta tuna da kungiyar Kwankwasiyya Singa Market, duba da rawar da take takawa wajen ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa a fadin jihar.

Haka zalika, Auwalu ya bayyana bukatar kungiyar ta samu sahalewar hukuma (notice) da za ta ba ta damar shiga cikin shirye-shiryen Gwamnati kamar yadda sauran kungiyoyi ke samu, domin kada a barsu a baya.

Ya kara da cewa kokarin da Gwamnatin jihar Kano ke yi na raya kasa ya cancanci yabo, yana mai rokon gwamnati da ta yi duba na tsanaki kan gudunmawar da kungiyar Kwankwasiyya Singa Market ke bayarwa wajen ci gaban jihar.

A karshe, ya ce lokaci ya yi da ya dace Gwamnatin jihar Kano ta tallafa wa kungiyar da jari, musamman ganin yadda take taimakawa wajen daukar marasa aikin yi tare da basu damar dogaro da kawunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kwalejin Audu Bako Ta Karyata Zargin Kin Bin Umarnin Gwamnatin Jihar Kano

Daga: Kabiru Getso Shugaban Kwalejin koyar da aikin gona ta Audu Bako da…

CSI T. Sa’eed Ya Sake Bada Kyautarsa Ga Hazikan Dalibai A S.P.S. Dawakin Tofa

Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa A kokarinsa na kara zaburar da dalibai…

Gwamnatin Jihar Kano Zata Hada Hannu Da Gwamnatin Tarayya Domin Ciyar Da Harkokin Sadarwa Na Zamani A Fadin Jihar

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya…

Kungiyar Jami’an Tsaro Na Sa Kai Tana Taka Rawar Gani Ba Tare Da An Sanyasu A Tsarin Biyan Albashi Na Kasa

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar Jami’an Tsaro na Sa Kai ta Kasa reshen…