Daga: Muhammad Adamu Abubakar
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi kudirori sama da 700 a cikin shekarar 2025, a matsayin wani ɓangare na ayyukanta na dokoki da sa ido kan harkokin mulki a jihar.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhaji Lawan Hussaini Chediyar Yangurasa, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da rahoton ayyukan majalisar na bana ga manema labarai a Kano. Ya ce daga cikin kudirorin da aka karɓa, majalisar ta amince da guda 15 waɗanda suka zama dokoki.

A cewarsa, dokokin da aka zartar sun shafi muhimman fannoni daban-daban na rayuwar al’umma. Daga cikinsu akwai dokar kafa Hukumar Dakile Yaɗuwar Cututtuka, Hukumar Kula da Tattara Bayanan Taswira, da kuma Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da ke kula da manyan allunan tallace-tallace a faɗin jihar.
Alhaji Lawan Hussaini, wanda ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala a majalisar, ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da kasafin kuɗin Jihar Kano da na ƙananan hukumomi na shekarar 2026, domin tabbatar da ci gaba da inganta rayuwar al’umma.
Har ila yau, ya bayyana cewa majalisar dokokin za ta fara amfani da sabon zaurenta a watan Maris na shekarar 2026, wanda aka gina domin ƙara inganta yanayin gudanar da ayyukan majalisar.
A ƙarshe, Shugaban Masu Rinjaye ya ce majalisar ta ɗage zamanta na wannan lokaci ne bisa rasuwar wasu ‘yan majalisa guda biyu, marigayi Alhaji Aminu Sa’adu Ungogo da marigayi Alhaji Aliyu Yusuf Daneji, inda ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta musu, Ya kuma ba iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.