Daga: Ibrahim Sani Gama

Sojojin Nijeriya sun ci gaba da samun nasarori a yaƙin da suke da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas.

A cikin makonni uku da suka gabata, dakarun rundunar “Operation Hadin Kai” sun hallaka sama da ‘yan ta’adda 600, ciki har da shugabannin Boko Haram da ISWAP.

Wannan nasarar ta samo asali ne daga ci gaba da kokarin kawar da ta’addanci tun farkon watan Yuni, bayan da ‘yan ta’adda suka kai hare-hare 12 a Jihar Borno, inda lamarin ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojoji da fararen hula da dama.

A makon farko na watan, sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 94.

Sai dai, an rasa jami’an tsaro 20, ciki har da sojoji da ‘yan sa-kai, yayin da wasu fiye da 20 suka jikkata.

Duk da wadannan nasarorin, har yanzu al’ummar yankin na ci gaba da rayuwa cikin fargaba saboda rashin tabbas da halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Garo Ya Wakilci Gwamna Abba A Taron Gwamnonin Arewa Da Majalisar Sarakunan Gargajiya

Daga: Mas’ud Mato Garo Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…

Jami’an Gwamnati Daga Bangarori Daban-Daban Na Kawo Ziyarar Ta’aziyya Gwamnatin Kano

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da…

Muna Samun Rashin Goyan Baya Daga Iyayen Matasa A Yakin Da Muke Da Matsalar Tsaro

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar rajin tabbatar da tsaro ta Tayani Mu…

Sabon Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta Jihar Kano, Tahir Ahmad Lawan, ya ziyarci sakatariyar karamar hukumar Dala, inda ya gana da shugaban karamar hukumar, Alhaji Suraj Ibrahim Imam.

Sabon Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta Jihar Kano, Tahir Ahmad Lawan,…