Sabon Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta Jihar Kano, Tahir Ahmad Lawan, ya ziyarci sakatariyar karamar hukumar Dala, inda ya gana da shugaban karamar hukumar, Alhaji Suraj Ibrahim Imam.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Kwanturola Tahir Ahmad Lawan ya bayyana cewa manufar zuwan sa ita ce tantance yadda jami’an shige da ficen ke gudanar da aikinsu a yankin, Kamar yadda ya kamata

A cewarsa, aikin Hukumar Shige da Fice ya haɗa da sa ido kan shige da ficen baki a faɗin jiha da ƙasar baki ɗaya, tare da wayar da kan jami’ai kan muhimmancin ƙara tsaurara bincike da kulawa kan ƙasashen waje da ke shigowa cikin ƙasar nan.

Haka Kuma Ya jinjinawa jami’an bisa kwarewarsu da jajircewarsu wajen gudanar da aikin su a Karamar Hukumar ta Dala.

Haka kuma, ya yaba wa shugabancin karamar hukumar Dala Alhaji Suraj Ibrahim Imam bisa goyon baya da haɗin kai da yake Baiwa Jami’an, yana fatan dangantakar za ta ci gaba da ɗorewa.

A nasa ɓangaren, shugaban karamar hukumar Dala, Alhaji Suraj Ibrahim Imam, ya nuna godiya bisa ziyarar, tare da tabbatarwa Kwanturolan cewa za su ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da ake bukata.

Ya kuma yabawa jami’in da ke kula da yankin, Hamid Abubakar, bisa ƙwazon da yake nunawa a aikinsa, yana fatan zai ci gaba da haka Dan Ciyar da Yankin gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kim Jong Un Ya Fara Nuna ’Yarsa Mai Shekara 13 A Matsayin Magajiyarsa

Daga: Abdullahi Bashir Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim…

Majalisar Dokokin Kano Ta Karɓi Kudirori Sama Da 700 A 2025

Daga: Muhammad Adamu Abubakar  Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi…

Shugaban Hukumar Alhazai ta Kano Ya Kai Ziyarar Duba Masaukin Alhazai a Makkah

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar…

Dangote Ya Rage Farashin Fetur, Ya Kaddamar da Sabon Tsarin Rarrabawa

Daga: Muhammad Adamu Abubakar  Kamfanin matatar mai na Dangote ya saukar da…