Daga: Mas’ud Mato Garo
Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shugaban cibiyar yada addinin musulunci ta Ganduje Foundation, Dr. Abdullahi Umar Ganduje tsohon gwamnan jihar Kano.
Da yake jawabi a wajen taron addu’o’in samun ingantaccen zaman lafiya, a jihar kano da najeriya, da kuma musuluntar da wasu mutane maza da mata da suka kar6i kalmar shahadar shigowa addinin musulunci su sama da dari uku da saba’in (370) da gidauniyar Ganduje Foundation ta musuluntar, ranar asabar din nan a gidan tsohon gwamnan dake miyangu jihar kano,

Gwamnan wanda mataimakin sa Alh Murtala Sule Garo ya wakilta, ya godewa jagoran cibiyar yada addinin musuluncin, Dr Abdullahi Umar Ganduje a bisa wannan muhimmin taro daya shirya tare da yi masa fatan karin samun karfin gwiwa kan wannan hidima da yake yiwa addinin musulunci.
Mataimakin gwamna Murtala Garo, ya kara da cewa, a madadin gwamna Alh Abba Kabir Yusuf, yana rokon Allah S.W.T ya tabbatar da wadanda suka musulunta akan wannan tafarki na addinin musulunci har karshen rayuwar su.

A karshe Garo ya karkare jawabin gwamna Yusuf, da Addu’ar nemawa kasa najeriya dauwamammen zaman lafiya da cigaban jihar kano, tare da godwa duk wadanda suka bada gudunmawa wajen wanzuwar wannan muhimmin abin alheri.
A nasa jawabin shugaban cibiyar yada addinin musulunci ta Ganduje Foundation, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yiwa najeriya da shugaban kasa fatan alheri da karuwar lafiya da zaman lafiya a kasa baki daya.
Ya kuma bayyana gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin Adalin gwamna mai aiki dare da rana da kuma son zaman lafiya ga al’ummar sa.