Kimanin Matasa ’yan Gwagwarmaya su goma sha biyar (15) ne Suka rabauta da samun tallafin babura daga Shugaban Karamar Hukumar Dala, Alhaji Suraj Ibrahim Imam, domin ƙarfafa ayyukansu da inganta rayuwarsu.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon tallafin baburan, Alhaji Suraj Ibrahim Imam ya bayyana cewa tallafin da aka bai wa matasan ’yan gwagwarmaya ba alfarma ba ce, illa cancanta , duba da irin gudummawar da suke bayarwa.
Yana Mai Cewar nan gaba kaɗan, za a ƙaddamar da wani tallafi na musamman ga mata 200 Dake Karamar Hukumar Dala.
A nata jawabin, Shugabar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Jihar Kano
Hajiya Sa’adatu Yusha’u Soja, ta yaba da wannan kyakkyawan shiri, tare da taya matasan da suka amfana murna. Ta jinjinawa Gwamnan Jihar Kano bisa yadda yake bai wa shugabannin kananan hukumomi cikakken goyon baya domin aiwatar da ayyukan da za su amfani al’ummar Kano.
Taron ya samu halartar Shugaban Karamar Hukumar Dawakin topa, Alhaji Anas Dan Maliki, da Mataimakin Shugaban karamar hukumar Dala alhaji Abdul’aziz Dayyabu Ahmad mai turare, kansuloli nadaddu da zababbu taron ya Gudana a Sakatariyar Karamar Hukumar ta Dala